Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KADUNA: Musulmi Da Kiristoci Sun Taya Juna Murnar Maulidi Da Kirisimeti


Groundhog Club co-handler Al Dereume holds Punxsutawney Phil, the weather prognosticating groundhog, during the 132nd celebration of Groundhog Day on Gobbler's Knob in Punxsutawney, PA
Groundhog Club co-handler Al Dereume holds Punxsutawney Phil, the weather prognosticating groundhog, during the 132nd celebration of Groundhog Day on Gobbler's Knob in Punxsutawney, PA

Bikin Kirismeti da na Maulidi ya zo kwana daya tsakani a duniya, inda Musulmi da Kiristocin Kaduna suka amsa gayyatar Fasto Yohanna Burru zuwa liyafar bikin Kirisimetin, inda shi kuma Faston da tawagarsa ke ci gaba da ziyarar taya Musulmi murnar watan Maulidi.

Hadin kai yana daya daga cikin abinda yake ciwa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya, musamman ma ta bangaren fahimta da mutunta addinin juna. Wanda masu tsokaci ke ganin hakan ne ma yake haifar da yawan fitintinun da ake samu tsakanin addinan kasar musamman Kirista da Musulmi.

Jihar Kaduna a Najeriya na daya daga cikin jihohin Najeriya da suka sha fama da wannan matsala ta dauki ba dadin maganar bambancin addini wanda hakan yayi sanadiyyar salwantar mutane da dama. Ga dukkan alamu wannan yanayi yana shudewa a hankali sakamakon abinda bahaushe ke cewa kan mage yaw aye.

Wasu masu fashin baki ma gani suke yi ‘yan siyasa na taka mummunar rawar gani sosai a maganar fadan addini don cimma manufofin siyasa bayan sun yi makadin na gal-gal, wato sun had aba tare da raba fadan ba.

Gayyatar Kiristoci zuwa yin buda baki da azumin watan Ramadan da bukukuwan Sallah, ko kuma gayyatar Musulmi halartar bikin Kirisimeti ya fara zama dabi’ar wasu shugabannin addinai a Kaduna irinsu Fasto Yohanna Buru, wanda ya hada liyafar da ya gayyaci musulmi taya su ci da sha a bikin Kirisimeti.

Bikin da ya zo kwana daya tsakaninsa da Maulidin Annabi Muhammadu tsira da aminci su tabbata a gareshi da aka yi ranar Alhamis, aka kuma yi Kirisimeti a jiya Juma’a, inda Kiristocin ke tunawa da Annabi Isa aminci ya tabbata a gareshi. Ga rahoton wakilin Muryar Amurka Nasiru Yakubu Birnin Yero.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG