WASHINGTON D.C. —
Shugaban kasar Algeria, Abdoulaziz Bouteflika ya yi murabus daga mukaminsa.
Ajiye mukamin nasa, na zuwa ne bayan da ma’aikatar tsaron kasar, ta yi kira ga dadadden shugaban da ya sauka cikin “gaggawa” bayan makonni shida da aka kwashe ana zanga zangar neman sauyin gwamnati.
Daruruwan mutane sun yi dandazo a wani Dandali da ke tsakiyar Algiers, babban birnin kasar, suka yi ta nuna farin cikinsu kan wannan mataki da shugaba Bouteflika ya dauka.
A yau Laraba, ake sa ran Majalisar Kundin Tsarin mulkin kasar za ta yi wani taro, na tsara yadda za a sauya gwamnatin.
Bisa tsarin dokar kasar ta Algeria, Kakakin majalisar dokokin ne zai zama shugaba na wucin gadi, inda za a ba shi wa’adin kwanaki casa’in ya shirya sabon zabe.
Facebook Forum