Gwamnatin ta Najeriya ta ce ta na tattaunawa ne da tsegerun tare da shiga tsakanin jami’an tsaro da kamfanonin mai.
Buhari ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin jakadan kasar Jamus, Michael Zinner da ke shirin kammala aikinsa a kasar.
A farkon makon nan rahotnanni sun ruwaito ministan harkokin matsa da wasanni, Barrister Solomon Dalung ya na cewa ya kai ziyara yankin inda ya gana da shugabannin kungiyar Niger Delta Avengers.
Sai dai kungiyar ta musanta wannan ikrarin ministan.
Ko a baya, gwamnatin ta Najeriya ta nemi tsegerun da su zo su hau teburin tattaunawa, amma suka bijire.
Amma Buhari ya ce gwamnatinsa a shirye ta ke ta yi dubi kan wasu yarjeniyoyi da gwamnatocin baya suka kulla da tsegerun a karkashin shirin nan na afuwa da aka musu.
Malam Musa Zubairu, mai fashin baki ne kan harkokin tsaro, kuma Jummai Ali ta tambaye shi yadda ya ke kallon lamarin: