A yayin tattaunawar ta da Archetypes tare da Fumudoh, Ba'amurkiya kuma ‘yar asalin Najeriya, Meghan ta ce ta yi wasu gwaje-gwaje na asali.
Ta ce, "Na nemi sanin tarihin zuriyata shekaru biyu da suka wuce," Fumudoh kuma ta ce: " Da gaske? Menene asalin ki?"
"Kashi arba'in da uku cikin dari ‘yar Najeriya," in ji Meghan.
Meghan ta bayyana cewa, makasudin faifan shine "bincike, da kuma karkatar da tamburan da ke kokarin hana mata cigaba." Babban abin da aka magance a cikin kashi na bakwai na jerin shirye-shiryen 12 shine na "Mace Bakar fata mai fushi."
Meghan ta gayyaci marubuciya kuma masanin ilimi Emily Bernard, 'yar wasan kwaikwayo da frodusa Issa Rae da mai gabatar da shirin Ziwe Fumudoh, don tattauna abubuwan da suka faru daban-daban game da wariyar launin fata da kuma yadda yake bayyana a rayuwar yau da kullum.
Meghan da kanta ta yi magana game da wariyar launin fata da ta fuskanta bayan ta sadu ta kuma auri mijinta Yarima Harry.
A farko- farkon soyayyar su a cikin 2016, Harry ya fitar da wata sanarwa daga Fadar Kensington ta hanyar sakataren sadarwa yana yin Allah wadai da "wariyar launin fata na kafofin sada zumunta da sharhin labarin yanar gizo," wanda aka yi wa Meghan.
Lokacin da ma'auratan suka kaura zuwa Amurka a cikin 2020 kuma daga baya suka tattauna abubuwan da suka faru na sarauta tare da Oprah Winfrey, batun wariyar launin fata ya sake tayar da hankali, gami da cewa wani dan gidan sarauta da ba a bayyana sunansa ba ya yi kalaman wariyar launin fata game da launi na yaran da za su haifa a nan gaba. .
A martanin da aka yi kan hirar su da Oprah, Fadar Buckingham ta ce "batutuwan da suka taso, musamman na wariyan launin fata, abun damuwa ne," ya kara da cewa "yayin da wasu tunowar na iya bambanta, sun dauke su da mahimmanci kuma dangin za su magance lamarin a sirrince."