Hukumomi a nahiyar turai na fadi-tashin ganin sun inganta fannonin kiwon lafiyar kasashensu, domin kaucewa yaduwar cutar coronavirus.
Jami'a a yankin sun ce akwai yiwuwar a samu masu dauke da cutar ba tare da wata alama da za ta nuna cewa suna dauke da ita, lamarin da suka ce zai iya kawo cikas wajen hana yaduwarta, ko da yake sun ce ba a samu tabbacin hakan ba.
Kasar Ukraine wacce har yanzu ba ta samu bullar cutar ba, ta dasa matakan tabbatar da “tsafta” a kan iyakokinta, inda duk wanda zai shiga kasar sai an dauki yanayin zafin jikinsa.
Sannan hukumomin Ukraine sun shawarci ‘yan kasar da su guji zuwa sauran kasashen nahiyar ta turai.
Sai dai kungiyar ta EU, ta ce babu wata nahiya da ta shirya wajen daukan matakan yaki da wannan cuta kamar nahiyar ta turai.