Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Girke Jami'an Tsaro a Majalisar Dokokin Najeriya


Wani mutum na wucewa ta kusa da motar 'yan sanda
Wani mutum na wucewa ta kusa da motar 'yan sanda

'Yan jam'iyya mai mulki ta APC na ganin, ya kamata ya yi murabus, tun da ya bar jam'iyyar, amma 'yan PDP suka ce ba za ta sabu ba.

Rahotanni daga Abuja, babban birnin Najeriya na cewa, an girke jami'an tsaron farin kaya na DSS a kofar shiga Majalisar Dokokin kasar.

Da safiyar yau Talata 'yan majalisu suka fara hallara a kofar majalisar, amma sai suka tarar da dumbin jami'an tsaro cikin kyakkyawan shirin ko-ta-kwana.

Wasunsu fuska a rufe, yayin da wasu kuma ake ganin fuskarsu.

Bayanai sun yi nuni da cewa, jami'an tsaron sun ce umurni aka ba su a lokacin da 'yan majalisar suka yi yunkurin shiga zauren majalisar amma abin ya cutura.

Sai dai daga bisani, an bar su sun shiga bayan da aka caje su.

Masharhanta na kallon wannan sabuwar takaddama a matsayin yunkurin da wasu 'yan majalisar ke yi na tsige shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki.

Shi dai Saraki ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP.

'Yan jam'iyya mai mulki ta APC na ganin, ya kamata ya yi murabus, tun da ya bar jam'iyyar, amma 'yan PDP suka ce ba za ta sabu ba.

Wasu masana shari'a sun ce babu wata doka da ta tanadi cewa lallai shugaban majalisar sai ya fito daga jam'iyya mai rinjaye a majalisar.

A halin da ake ciki, jami'iyyar APC da abokiyar hamayyarta ta PDP na ikarin cewa su suka fi rinjaye a majalisar.

A makon da ya gabata ne wasu 'yan majalisar dokokin ta Najeriya da dama suka fice daga APC zuwa PDP.

Wannan matakin ya haifar da muhawarar wanda ya fi rinjaye a majalisar..

Sa-in-sar na faruwa ne a daidai loakcin da majalisar ke shirin wani zaman gaggawa wanda zai yi dubi kan kasafin kudin da ke gaban majalisar na biliyan N242 da shugaba Buhari ya gabatar.

Za a yi amfani da kudin wajen gudanar da zaben badi kamar yadda jaridun kasar da dama suka ruwaito.

Shugabannin majalisun, za su gana ne tare da shugabannin hukumar zabe na INEC, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a shafin yanar gizonta daga wata majiya da ba ta bayyana sunanta ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG