Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhimmancin Zuwa Awo Ga Mata Masu Ciki


Mata masu ciki.
Mata masu ciki.

Bisa ga masana, abu ne mahimmi ga mata masu ciki, ko kuma tsammanin yin ciki, su shirya domin yin rijistar gwajin ciki da wuri domin cikakkiyar lafiyar ‘ya’yansu.

Bisa ga masana, abu ne mahimmi ga mata masu ciki, ko kuma tsammanin yin ciki, su shirya domin yin rijistar gwajin ciki da wuri domin cikakkiyar lafiyar ‘ya’yansu. Ziyarar mata masu ciki na hadawa da allurar rigakafi rinku, bincike da yin magani ga kowacce cuta, da kuma duba wasu alamu a lokacin ciki. Ana gwada mata masu ciki a lokacin awo domin sanin ko suna da wadansu cututtuka a kuma yi masu jinya domin kare jariransu.

Wani kwararren likitan kananan yara a sashin koyarwa na lafiyar yara, a jami’ar asibitin koyarwa na Obafemi Awolowo Dr. Jerome Elusiyan, ya baiyyana wannan zuwa gwajin mata cewa, mace mai ciki nayin wannan domin lafiyar cikinta da kuma wanda take shirye da nakuda da ke zuwa kowanne lokaci, da kuma sakamakon ciki mai kyau.

Da yake hira da wata mujallar kiwon lafiya, Dr. Elusiyan yace matsalolin da ake samu na haihuwa kamar su zazzabin da hawan jinni na mai ciki da kuma wani yanayi dake sa jarirai su kasa yin lumfaashi bayan minti daya na haihuwa, za’a iya kiyaye shi ta wurin zuwa awon ciki. Kuma bisa ga Elusiyan, jarirai da suka sami wannan matsalar na iya mutuwa ko su sami wani ciwo wanda yake kama da farfadiya da sauransu. Ya kara cewa wannan gwajin yana hadawa da ilimi da yin bayani ga mata dake da alamun matsaloli gare ta da kuma jaririnta, wanda za’a iya yin shirin kare ta daga gare su.

Sai dai abin bakin ciki shine mata da yawa basu kula su rika zuwa awo.

Bincike ya nuna cewa cikakkun bayanai na kasa sun nuna tsakanin kashi 5 da 10 na dukan yara na Africa suna girma da nakasa da yawa. Babban dalilin wannan nakasar – hadi da irin yanayin jikinsu shine matsaloli lokacin haihuwa – hadi da cutar shan inna, kyanda, sankarau, zazzabin malariya na kwalwa, da kuma rashin zuwa awo da da rashin abinci isasshe da sauransu.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG