Masana a fannin shari’a sun ce bayyana kadara da kundin tsarin mulkin kasa ya umurci manyan jami’an gwamnati su yi na da tasiri matuka domin kafa ce ta hana yin almundahna da dukiyar kasa.
Sai dai wasu na ganin hukumar da aka damkawa alhakin kula da wannan fannin ba kasafai ta ke gudanar da ayyukanta yadda ya kamata ba.
A tsakiyar makon da ya gabata ne shugaba Muhammadu Buhari da mataiamakinsa Farfesa Yemi Osibanjo suka bayyana dukiyar da suk mallaka yayin da gwamnatinsu ke cika kwanaki 100 da kama ragamar mulki.
“Abu ne wanda ya ke cikin tsarin mulki, wanda aka bawa hukumar da ke kula da wannan fanni su aiwatar, amma sai dai abubuwan da suka gabata a baya, ba a binsu, abubuawan da ya kamata ayi ba a yi.” In ji Barrister Baba Shaba, wani lauya mai zaman kansa a Abuja.
To ko menene ya sa a baya ba a bin wannan doka? Barrister Shaba ya ce “Ba wnai abu ne, kowa ya san yadda shugabannin baya suka kasance masu taka doka, za ka taka doka, kuma ba abinda za a maka.”
To amma shin ko hakan na nufin hukumar da ke kula da wannan fannin na bayyana kadara ba ta da amfani ke nan? Sai ya ce “tana da tasiri, domin mun ga yadda abubuwa suka faru lokacin da aka kira Bola Tinubu, mun san cewa siyasa ce, amma mun san cewa tana da tasiri idan tana so ta zama mai tasiri.”
Yadda Ake Tantance Kadarorin Jami’an Gwamnati?
Hukumar da ke kula da fannin bayyana kadarori, ta ce yadda ta ke tantance irin bayanan dukiyar da aka fitar shi ne ta hanyar gayyatarsu jami’an gwamnatin, domin su zo su yi bayani dalla-dalla.
Hukumar ta kara da cewa, ta na kuma zuwa ta je ta binciki asusun jami’an, ta duba ko adadin kudin da mutum ya bayyana ya yi daidai.
“Haka kuma mukan fita mu je mu duba bayanan filaye ko gidajen wadannan jami’an domin mu tabbatar, abin da ya ke zama mana kalubale shi ne rashin wadatar kudaden gudanarwa, amma hakan ma baya hana mu gudanar da ayyukanmu kamar yadda doka ta umarce mu yi.” In ji Jami’ar hulda da jama’ar hukumar Mrs. Iyabo.
PDP Ta Soki Buhari da Osinbajo
Sai dai babbar Jam’iyyar adawa a Najeriyar ta PDP ta soki matakin da shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo suka dauka na bayyana kadarorinsu.
A cewar PDP, hakan da suka yi wani salo ne na share fagen komawa kan karagar mulki a shekarar 2019 domin a cewarsu akwai lauje a cikin nadi.
Jam’iyyar ta PDP ta ce menene fa’idar bayyana cewa shugaba Buhari yana da gidaje guda hudu, ba tare da ya fadi darajarsu ba, tana mai jaddada cewa bayyana biyu daga cikin gidajen a matsayin na laka bai isar ba.