Ministan ruwa baring ado Injiniya Suleman Hussaini Adamu ya bayyana mana irin ayyukan da ya yi a ma'aikatar sa ta kula da ruwa a Najeriya. Sai dai ministan ya ce abu mai muhimmancin shine y agama aikin sa lafiya, kamar yanda yake sa ran sauran takwarorin aikin sa ma sun kawo karshen aikin su lafiya.
Injiniya Suleman ya ce a cikin shekaru uku da rabi da ya yi aiki a matsayin minista, mutane sun tabbatar masa ma'aikatar sa ta sauya salon aikin ta kuma ta samu ci gaba ainun,ba kamar lokutan da suka shude ba, inda aka mayar da ita tankar saniyar tatsa. Ministan ya ce a baya ma'aikatar ruwa ta Najeriya bata fara aiki ta karasa, kana tana husknatar matsaloli wurin bada kwangila, lamarin da ya yi sanadiyar tabarbarewar samar da ruwa a Najeriya.
Ministan ruwa a Najeriya, ya bayyana nadamar san a rashin samun damar kafa dokar ruwa a Najeriya tsakanin lokacin da ya yi aiki. Ya ce dokar ta samu amincewa majalisar wakilai amma ta gaza cimma buri yayin da aka gabatar da ita a majalisar dattawa, inda aka sa siyasa a cikin lamarin.
Ministan ya kara da cewa wata babbar matsala da hukumar ruwa ta husaknta a lokacin aikin sa itace yanda ake kasafin kudin hukumomin raya koguna a Najeriya, inda aka maida hukumar mai raba kwangila. Hakan ya addabi kokarin da ya yi na inganta wannan hukuma. Ya ce ‘yan majalisa sun saka wadannan ayyukan hukumar raya kogunan a cikin ayyukan da ake gudanar da su a mazabu wanda basu da alaka da su.
Wakilin mu Hassan Maina Kaina daga Abuja yana dauke da ci gaban hirar da ya yi minitsan ruwa:
Facebook Forum