Batun sauya sheka al’amari ne daya zama ruwan dare a tsakanin ‘yan siyasa a Najeriya tun gabanin jam’iyyun siyasar kasar su fara gudanar da zaben fitar da gwani domin tunkarar zaben shekara ta 2019. Sai dai masana kimiyyar siyasa na ganin hakan koma baya ne ga ci gaban dimokaradiyyar kasar.
Tun bayan da Najeriya to koma tafarkin dimokaradiyya kusan shekaru 20, manya, matsakaita da kananan ‘yan siyasa ke sauya sheka daga wannan Jam’iyya zuwa waccan.
Na baya bayan nan sun hada da gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal da Sanata Sulaiman Hunkuyi da Sanata Bukola Saraki da Yakubu Dogara da Alhaji Ahmed Musa Ibeto tsohon jakadan Najeriya a Afrika ta kudu, haka kuma da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dukkanin su daga Jam’iyyar APC zuwa PDP, yayin da Sanata Godswill Akpabio ya kaura daga PDP zuwa APC.
Bayan sauya sheka wasu ‘yan siyasar kanyi katari su dace bukata ta biya, wasu kuwa su gamu da akasin haka. Dakta Ahmed Salik tsohon dan majalisar tarayya ne daga jihar Kano, rashin yin adalci a jam’iyya shine babban dalilin da yasa suka yi ta sauya sheka.
Sai dai masu iya Magana kan ce ba duka akan taru a zama daya ba, Sanata Mas’udu El-Jibril Doguwa dan Jam’iyyar PDP ne tun kafa shekaru 20 baya, kuma yana ganin tsalle-tsalle a siyasa baya haifar da ‘da mai ido. Haka kuma babu abin da yake taimakawa dimokaradiyya wajen ci gaba.
A cewar masana kimiyyar siyasa, baya ga nuna rashin akida, tsalle daga wannan jam’iyyar zuwa wata na haifar da mummunan koma baya ga demokaradiyyar Najeriya.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum