Yayin da kasashe a fadin duniya ke shirin ba da dama ga masu yawon bude ido shiga kasashensu, hukumar kula da harkar sufurin jiragen sama ta Majalisar Dinkin Duniya ICVO, ta yi gargadi da a dau matakan kariya a harkar tafiye-tafiyen jiragen sama.
ICVO ta fadi cewa za’a gwada zafin jikin matafiya da zarar sun shiga filin tashin jirage, kuma su kasance ba sa dauke da kaya masu yawa sannan za su saka takunkumin rufe fuska da baki a cikin jirgi da kuma yayin da su ke harabar inda ba za’a iya tabbatar da tazara tsakanin matafiya ba.
Daga cikin matakan, za’a samawa masu aiki a cikin jirgi kayayyakin kariya ciki har da takunkumi da safar hannu.
A Amurka, gwamnati ta ce mutum 26,000 su ka mutu sanadiyyar COVID-19 a gidan kula da tsofaffi, kusan kaso daya bisa hudu na adadin wadan da su ka mutu da cutar.
Kimanin Ma’akatan wadannan gidaje 450 suka mutu daga cutar.
Facebook Forum