Dubban mutane ne su ka bazama kan tituna a kasar New Zealand a yau Litinin, suna nuna goyon bayan Amurkawa a zanga-zangar nuna alhininsu akan kisan Ba'amurke bakar fata George Flyod, yayin da ya ke hannun ‘yan sanda.
Masu zanga-zangar a birnin Auckland sun yi tattaki zuwa ofishin jakadancin Amurka, su na masu rera wakoki irin wadanda ake rerawa a Amurka da cewar “Rayuwar bakaken fata na da muhimmanci” da kuma cewar “Idan har babu adalci to babu zaman lafiya.”
Zanga-zangar ta yau ta biyo ne bayan wasu da aka yi jiya Lahadi a kasashen Birtaniya, Brazil, Canada, da dai sauran kasashe.
Dubban mutane ne suka tattaru a tsakiyar birnin Landon, domin nuna goyon bayan su ga Amurkawa da su ka fito domin yin Allah waddai da abun da jami’an ‘yan sanda ke yi, tun bayan mutuwar George Floyd a makon da ya wuce a birnin Minneapolis, da ke jihar Minnesota.
Floyd ya mutu ne bayan dan sanda farar fata Derek Chauvin ya danne wuyansa da gwiwar kafarsa fiye da tsawon mintuna 8, duk kuwa da cewar Floyd yayi ta maimaita cewar baya iya numfashi.
A kasar Denmark mutane sun yi zanga-zanga zuwa ofishin jakadancin Amurka da ke Copenhagen a jiya Lahadi, suna dauke da alluna da rubutun cewar “A daina kashe bakaken fata.” Haka ma a kasar Jamus, masu zanga-zangar sun rike alluna da rubutun cewar “A tuhumi jami’an tsaro da laifin da suka aikata” da kuma “wa zaku kira a lokacin da ‘yan sanda suka yi kisa?
Facebook Forum