Tun daga ranar daya ga kowane watan Fabrairun duk shekara Majalisar Dinkin Duniya ke kawo fahimtar juna tsakanin addinan duniya da shugabanninsu.
Manufar majalisar shi ne a samu kyakyawar fahima tsakanin manyan addinai tare da mutunta juna da hakan ka iya kawo zaman lafiya tsakanin al'umma.
Wani mai bishara Kutiya Zarma a jihar Adamawa yace makon da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin kawo fahimta tsakanin addinai ya nada mahimmanci kwarai ganin cewa abun da za'a iya yi a duniya shi ne hada kawunan addinai. Manufar ita ce a gani sun zauna lafiya ba tare da tsangwamar juna ba.
Shi ma Shaikh Abdullahi Isa Adam babban limamin masallacin ATBU Yola ya amince da mahimmancin makon inda ya bada misali da abub dake faruwa a kasar Malaysia. Yace "mu tsaya mu yi addininmu tsakaninmu da Allah domin bauta masa. Wancan mai addini daban shi ma ya yi irin nasa.Kamar kasar ta Malaysia akwai addinai hudu masu karfi amma kowane na yin nasa ana kuma mutunta juna ba tare da nuna wariya ba ko tsangwamar kowa ba.
Ga karin bayani