Ofishin da ke kula da kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kira ga gwamnatin Mali da ta gudanar da bincike kan kisan mutum sama da 150 da aka yi a kasar tare da gurfanar da masu hannu a wannan aika-aika.
Ofishin da ke kula da kare hakkin bil adaman, ya ce wannan hari da aka kai a ranar Asabar a Ogossagou a yankin Mpoti da ke tsakiyar kasar ta Mali, ya nuna yadda matsalar fadace-fadace ke karuwa a kasar.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce, cikin ‘yan shekarun da suka gabata, fada tsakanin Fulani da ‘yan kabilar Dogon, ya yi sanadiyyar mutuwar mata da kananan yara da maza da yawansu ya kai 600.
Rikicin wanda ya kazanta a baya-bayan nan, kan samo asali ne daga takaddama da ake yi kan filaye da ruwa tsakanin Fulani wadanda makiyaya ne da ‘yan kabilar Dogon wadanda mafarauta ne.
Ofishin da ke kare hakkin bil Adama Majalisar Dinkin Duniya ya ce, wadanda suka tsira daga harin da aka kai a ranar Asabar, aksarinsu Fulani ne, wadanda suke zargin ‘yan kabilar Dogon da kai musu hari da manyan bindigogi.
Mai magana da yawun ofishin na Majalisar Dinkin Duniya, Ravina Shamdasani, ta ce wasu daga cikin ‘yan kabilar ta Dogon, suna kallon Fulanin a matsayin masu goyon bayan kungiyoyin mayakan da ke ikrarin jihadi.
“Na fahimci cewa, da yawa daga cikin al’umomin, sukan fake ne da fadan kabilanci, ko kuma suka fake da cewa suna kare kansu ne. Sukan dauki doka a hannunsu domin kawar da wadanda suke wa kallon abokan gaba da ake masu kallon masu tsattsauran ra’ayi, wanda hakan kan kare akan yara kanana da ake kashewa, ka ga har ana jefa gawar mutane a rijiya ko a kona mutane da ransa a gidajensu.” Inji Shamdasani.
Shamdasani ta ce ta kula, ‘yan kabilar ta Dogon ne kadai ke zargin cewa Fulanin na nuna goyon baya ga mayakan da ke ikrarin jihadi.
Ta kara da cewa, gwamnatin Mali ta kaddamar da wani bincike sannan ta kama mutane a baya, a wani yunkuri da ta yi na kawo karshen rikicin, amma ta ce babu ko mutum guda da aka gurfanar a gaban kotu.
Shamdasani ta kara da cewa, yanzu haka sun tura wata tawaga mai dauke da masu binciken manyan laifuka da masu kare hakkin bil’adama zuwa kauyukan da aka kai hare-haren, tana mai cewa za su tattauna da mazauna yankin domin gano asalin abin da ya faru.
Ta kuma kara da cewa, ofishin da ke kare hakkin bil adam ana majalisar, zai goyi bayan gwamnatin Mali domin ta fadada bincken.
Facebook Forum