A yayin da sojojin Afrika ta Kudu da na India ke taimakawa wannan aiki a wani shawagi ta sama domin neman mutane da suka bata, sojojin sun huskanci matsaloli wurin taimakawa dubun dubatar mutane dake kasa.
Ministan filaye da muhalli na kasar Mozanbique Celso Correia yace har iyau lamarin akwai wuya, amma dai zai inganta. Yace akwai mutane 1,500 dake kan rufin gidaje da bishiyoyi dake tsananin bukatar taimako da kana wasu mutane dubu 89 dake zaune a sansanonin.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, jumular wadanda suka mutu a Mozambique da Zimbabwe da Malawi ya kai mutane 700. Ma’aikatan ceto sun ce lallai ne adadin zai karu, yayin da ruwan ambaliyar ke janyewa. Kimanin mutane miliyan daya da dubu 700 ne lamarin ya shafe su, bala’i mafi tsanani da ya addabi yanki a cikin shekaru da dama.
Facebook Forum