Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban Mutane Ke Tsallaka Kan Iyakar Chadi Don Gujewa Yaki A Sudan - MDD


Mutane da ke tsallakawa kan iyakar kasar Chadi daga makwabciyarta Sudan domin gujewa tashin hankalin
Mutane da ke tsallakawa kan iyakar kasar Chadi daga makwabciyarta Sudan domin gujewa tashin hankalin

Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce da yawa daga cikin mutanen da suka taho daga Darfur sun samu munanan raunuka sakamakon rahotannin da ke cewa ana kai wa fararen hula da ke tserewa hari da gangan tare da karuwar kabilanci ga tashin hankalin.

Hukumar samar da abinci ta MDD ta ce dubban mutane ne ke tsallakawa kan iyakar kasar Chadi da ke tsakiyar Afirka daga makwabciyarta Sudan domin gujewa tashin hankalin da aka kwashe kusan watannin uku ana yi wanda babban jami’in jinkai na duniya ya bayyana a matsayin yakin basasa mafi muni.

Wasu yaran da suka tsallakawa daga Darfur zuwa Chadi na fama da rashin abinci mai gina jiki
Wasu yaran da suka tsallakawa daga Darfur zuwa Chadi na fama da rashin abinci mai gina jiki

Hukumar samar da abinci ta duniya ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar yau Talata cewa, mutane dubu 20,000 daga yankin Darfur na kasar Sudan sun isa karamin garin Adre da ke kan iyakar kasar Chadi a cikin makon da ya gabata kadai.

Hukumar ta ce da yawa daga cikin mutanen da suka taho daga Darfur sun samu munanan raunuka sakamakon rahotannin da ke cewa ana kai wa fararen hula da ke tserewa hari da gangan tare da karuwar kabilanci ga tashin hankalin.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce kimanin kashi 10 cikin 100 na yaran da ke tsallakawa daga Darfur zuwa Chadi na fama da rashin abinci mai gina jiki.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG