Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mazauna Sansanin Mutanen Da Suka Rasa Muhallansu A Sudan Ta Kudu Sun Bukaci A Dakatar Da Shugaban Kamitin


Wasu mazauna sansanin mutanen da suka rasa muhallin su a kasar Sudan ta Kudu, sun bukaci a kori shugaban kwamitin sa ido a yarjejeniyar samar da zaman lafiya da aka cimmawa a shekarar 2015 daga bakin aiki.

Mutanen sun soki lamirin Festus Mogae, wanda shine ya shugabanci kwamitin hadin gwiwa da tantancewa na kin bada bayanin abinda gwamnati tayi game kin bin umurnin da aka cimmawa na dakatar da bude wuta, da kuma kashe-kashe, fyade, azabtarwa da sojojin gwamnatin kewa farar hula.

Kwamitin na hadin gwiwa ya bada rahoton cewa duka sassan biyu kowa ya taka rawar kin bin umurnin da aka cimmawa game da yakin na kasar Sudan Ta Kudu.

Mazauna sansanin suka ce Mogae yaki ya bada cikakken bayanin halin damuwar da daruruwan farar hular da suka yi hasarar matsugunnin su sakamakon yakin da ya barke a kasar ta Sudan ta Kudu, suke ciki.

Wani shugaban al’umma mai suna Bikan Kuol, dake wannan sansanin yace baya da sauran wani kwarin gwiwa ga shugaban na hadin gwiwa domin ko ya gaza aiwatar da aikin da aka damka masa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG