Amurka ta nuna damuwarta akan yadda bangaren gwamnatin Kwango-Kinshasa da na gamayyar jam’iyyun ‘yan adawa suka kasa aiwatar da yarjejeniyar sauya ragamar mulkin kasar da suka rattabawa hannu a watan Disambar bara bayan watanin da aka kwashe ana dauki ba dadi a kasar.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta dora laifin akan bangarorin biyu saboda gazawar da suka yi wajen cimma matsaya akan yarjejeniyar, wacce ta hada da nadin sabon firai minista.
“Kasa aiwatar da yarjejeniyar na nuna dakilewa ‘yan kasar Kwango muradunsu kuma ya kawo tsaiko ga cigaban da aka samu a kasar ya zuwa yanzu" a cewar kakakin ma’aikatar harakokin wajen Amurka, Mark Toner.
Ya kamata shugaba Joseph Kabila ya sauka daga kan karagar mulki tun ranar 19 ga watan Disambar shekarar da ta gabata, wato karshen wa’adinsa na biyu, amma kuma aka dage zaben shugaban kasan da ya kamata ya maye gurbinsa kuma har yanzu Kabila na nan a matsayin shugaba.
Facebook Forum