Yayin da suka kama aiki a jiya litini, wakilin sashen Hausa na muryar Amurka a jamhuriyar Nijer, Sule Mumuni Barma, ya tuntubi daya daga cikinsu Hon, Maman Isa, mataimakin shugaban jam’iyyar MODEL-Lumana, yankin maradi inda ya bayyana cewa;
“Mun san wannan lamari dai Allah ne ya kawo shi, kuma shi yayi maganin komai, ni ba bakon majalisa bane, kowa yasan cewa akwai siyasa cikin lamarin amma mun bar komai a wurin mai kowa mai komai”.
Jam’iyyar MODEL-Lumana, madugar jam’iyyun adawar Nijer, na alfahari da komawar wadannan kusoshi nata cikin zauren majalisa kamar yadda Hon, Ahmed Ben Hamada, dan majalisar dokokin kasar daga mazabar yankin Diffa ya bayyana.
Jam’iyyar MNSD-Nassara, wadda hukumomi suka cafke daya daga cikin kusoshinta na Maradi, Alhaji Sani Bala, a yayin da ake gudanar da farautar wadanda ake zargi da yunkurin kifar da gwamnatin kasar a jajibirin zaben shekarar 2016, na cewa ya kamata ‘yan siyasar kasar su mayar da lamarin siyasa na siyasa domin ciyar da kasar gaba kamar yadda Hon, Lamido Mumuni Haruna ya yi wannan gargadi.
Hon, Mamman Isa, ya tabbatarwa talakawan kasar cewa ba gudu ba ja da baya a maganar gwagwarmayar nemar masu ingancin rayuwa. Kama aikin wadannan ‘yan majalisar dokoki da wasu daga cikin abokansu ke wa lakabi da ‘yan kason siyasa, ya zo dai dai da lokacin da majalisar dokin kasar ke cika shekara guda da soma aiki.
Daga Yamai ga rahoton Sule Mumuni Barma.
Facebook Forum