A wani mataki na kaucewa harin da ake shirin kai wa, mutane suna ta tserewadaga Mekele, babban birnin yankin Tigray da ke Ethiopia, bayan umarnin daFirai minista Abiy Ahmed ya bayar na aiwatar da "matakin sojina karshe" akan dakarun yankin na Tigray.
Abiy ya gargadi mazauna Mekele ranar Alhamis da su kwance damara su kuma kasance a cikin gidanjensu yayin da aka umarci rukunin sojoji su kutsa kai.
Amma gwamnatinsa, ta ce za ta kare fararen hula.
A halin yanzu, abinci da sauran abubuwa bukatun yau da kullum suna sun fara karewa a yankin Tigray da ke da mutum miliyan 6.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a hanzarta kai kayan agaji ba tare da nuna banbanci ba.
An kashe daruruwan mutane yayin da sama da dubu 40,000 suka tsere zuwa Sudan da ke makwabtaka da yankin, inda suke ba da labarin mummunan tashin hankalin da suka fuskanta.
Rikicin ya tayar da hankalin kungiyoyin kare hakki da bil adama da kuma Majalisar Dinkin Duniya, wadanda suka bukaci Abiy da ya nemi hanyar diflomasiyya don magance matsalar, lura da irin wahalhalun da fararen hula ke ciki, wadanda sun riga sun tagayyara sanadiyyar raunin tattalin arzikinsu da kuma annobar coronavirus.