Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, sun yi kira ga dakarun kasar Ethiopia da su kiyaye lafiyar fararen hula a yankin Tigray, yayin da wa’adin mika-wuya da gwamnati ta sakawa dakarun yankin ke karatowa.
Firai Minista Abiy Ahmed ya ba dakarun neman ‘yancin yankin na Tigray da ake kira TPLF nan da zuwa gobe Laraba, da su mika wuya ko kuma birnin Mekele ya fuskanci mamayar soji.
A ranar Litinin dakarun Ethiopia suka ce, sun yi wa birnin na Mekele kawanya da tazarar kusan kilomita 50.
Shugaban yankin Tigray Debretsion Gebremichael ya musanta ikrarin dakarun Ethiopian, yana mai cewa kokari kawai suke su yi rufa-rufa kan gazawarsu.
Katse layukan sadarwa, ya sa tabbatar da rahotonni daga yankin ya zama abu mai wuya yayin da aka kwashe mako uku ana ba ta kashi a yankin.