Manyan jamia'an kurdawan suka ce sojojin ne yanzu keda ikon kauyukan dake sassan birnin na Sanjir da kuma manya-manyan titunan dake da mahada da Masul dake arewacin Mosul inda 'yan tawayen na ISIS ke dauka a matsayin babban birnin su wanda yake kudancin Raqqa dake Syria.
Hanyar wadda aka fi sani da Highway 47 ita ce 'yan kungiyar ta ISIS ke bi domin safaran makaman su , dama ma duk da wani sauran abin masarufin da suke anfani dashi wajen wannan yakin.
Kamar yadda rundunar ta Amurka tace zata tabbatar ta kara kaimi domin ganin sojojin nata sun kara takurawa mayakan na ISIS ta yadda zasu raba wa mayakan na ISIS hankali.
Mai Magana da yawun ma'aikatar tsaro ta Amurka Peter Cook ya bayyana harin na jiya a matsayin wata nasarar hadin gwiwa ce tsakanin masu bada shawara na Amuka da mayakan Kurdawan na Iraqi.
Yace yana mai kwarin gwiwar cewa samun nasarar kamr wannan hanyar zata kara durkusad da kokarin yan kungiyar ta ISIS musammam a arewacin Iraqi