Jami’an tsaron Kenya guda takwas mayakan kungiyar Al Shabab suka kashe a ranar Lahadi a karamar hukumar Wajir dake arewa maso gabashin kasar. Wannan yankin ya sha fama da hare haren yan yakin sa kai dake tsalaka kan iyaka daga kasar Somaliya.
Su dai jami’an tsaron suna sintiri ne a lokacinda aka kai musu hari kusa da garin Bojigaras.
Hukumomi sun bayyana cewa motar jami’an tsaron ce ta taka nakiya. Bayan nakiyar ta yi bindiga, sai mayakan kungiyar Al Shabab da suka boye suka bude musu wuta. Nan take suka kashe duk jami’an sai soja daya wanda shi ma ya cika a asibiti.
Maharan sai suka arce suka doshi kan iyakar kasar da Somaliya. Isa Ahmed wani dan Majalisar karamar hukumar Wajir ya ce mazauna yankin sun nuna damuwar su kafin harin, kuma sun yiwa jami’an tsaro bayani, amma basu dauki wani mataki ba.
Yace da wannan jami’an tsaro sun amsa kiransu ne cikin gaggawa da al’amari bai faru ba, ko kuma da anyi Rigakafi. Tun farko mayakan sa kan sun sanar da jama’ar yankin su kuma suka tseguntawa jami’an tsaro cewa akwai yan yakin sa kai a yankin. Kazalika an fadawa jami’an tsaro maharani sun sha alwashin daukan matakin da ‘yan yankin zasu yi da na sani
Facebook Forum