Bayan tattaunawarsu yau asabar a Magadishu, shugabannin sun fada a wata sanarwa cewa, kasashen biyu zasu inganta harkokin diplomasiya da kuma na cinikayya tsakaninsu da ya hada da bude ofisoshin diplomasiya da kuma kauda dukan shigayen cinikayya da na tallatin arziki.
Shugabannin sun maida hankali kan ci gaban tattalin arziki da kuma zuba jari da nufin samar da kyakkyawar makoma ga al’ummarsu da kasashen yankin kuryar arewa maso gabashin Afrika, da kuma nahiyar Afrika baki daya.
Ahmed shine shugaban kasar Habasha na biyu da ya taba kai ziyara Somalia. A shekara ta dubu biyu da bakwai, tsohon Firai ministan kasar Ethiopia Meles Zenawi ya kai ziyara Mogadishu bayanda sojojinsa suka taimakawa gwamnatin Somaliya ta hambare mulkin kungiyar kotunan Islama da ta mallaki ikon babban birnin kasar na dan lokaci.
Kasar Habasha tana da sama da dakaru dubu hudu da dari biyu dake aiki karkashin shirin wanzar da zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Afrika a Somalia
Facebook Forum