Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za a Damke Barayin Gwamnati a Kenya


Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta

Yayin da almundahana ke barazana ga kasar Kenya, Shugaba Uhuru Kenyatta ya yi kukan kura zai dira kan barayin gwamnatin.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya kara azama a yakin da ya ke yi da almundahana, ta wajen bayar da sanarwar cewa kowane jami'in gwamnati zai fuskanci binciken tantance irin rayuwar da ya ke yi don a san inda ya samu dukiyarsa. Wannan sanarwa ta baya-bayan nan, ta biyo bayan wani rahoton dabaibaye kasar da almundahana ta yi, ta yadda aka sace miliyoyin daloli daga cibiyoyin gwamnati.

Shugaba Kenyatta ya yi tayin zama na farko da za a yi masa irin wannan bincike da zummar gano jami'an gwamnati da ke satar, ya na mai cewa wannan binciken yanayin rayuwar ma'aikatan, zai taimaka wajen dakile almubazzaranci da dukiyar al'umma. Ya ce kowani ma'aikacin gwamnati zai bayyana inda ya samu dukiyarsa.

"Sai ka gaya ma na cewa, wannan ne gidana, albashi na kaza ne, ga kuma yadda na gina gidan. Kuma ko da ka sayi mota da sunan matarka ko danka, sai mun gane motarka ce, kuma za mu tambaye ka yadda ka saya. Dole ka yi bayani. Kuma da ni za a fara wannan binciken salon rayuwar." a cewar Shugaba Kenyatta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG