Kungiyar alarammomi mahaddatan Kur'ani reshen jihar Neja ta gudanar da wani babban taronta a Minna, fadar gwamnatin Neja.
Mahalarta taron sun yi Allah wadai da ayyukan kungiyar Boko Haram mai tayar da hankalin al'ummar Najeriya. Sun kuma nuna rashin jin dadinsu akan yadda dabi'ar yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ke kara ta'azzara.
Alaramma Musa Adamu Hadeija sabon shugaban kungiyar a jihar Neja ya ce yana son al'umma su sani cewa abubuwan da kungiyar Boko Haram ke yi da suka alakanta su da addinin Musulunci, ba addinin Musulunci ba ne.
Shi ma sakataren kungiyar Adamu Abdullahi Idris ya ce fashi da makami da yin garkuwa da mutane, injishi addini ya ce a kashesu.
Kungiyar ta tabo batun matsalar yawon bara da yara kananan ke yi da ta yiwa arewacin Najeriya katutu. Kungiyar zata bada gudummawa domin shawo kan al'amarin.
A saurari rahoton Nasiru Mustapha Batsari da karin bayani.
Facebook Forum