Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Yada Labaran Karya Da Furuci Mai Harzukarwa a Najeriya


Ministan Yada Labaran Najeriya, Lai Mohammed.
Ministan Yada Labaran Najeriya, Lai Mohammed.

Masu ruwa da tsaki a harkar yada labarai sun bukaci al’ummar Najeriya su guji yin furuci masu harzukarwa da yada labaran ‘karya don a samu hadin kai a ‘kasa.

An gudanar da wani taron koli na musaman da ya hada masu ruwa da tsaki a harkar yada labarai daga jihohi 36 na Najeriya, mai taken ‘Furuci Masu Harzukarwa Labaran ‘Karya da Hadin Kan ‘Kasa’.

Masana a harkar yada labaran sun tattauna kan barnar da irin mugayen kalamai da wasu ke amfani da kafafen yada labarai wajen harzuwa zamantakewar al’ummar Najeriya.

A cewar Ministan yada labaran Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, dole ne ‘yan Najeriya su gujewa furuci masu tsauri dake harzuka al’umma da haddasa rabuwar kawuna a kasar.

Manufar taron shine tattaunawa don warware matsalar yada labarai a Najeriya,

Domin karin bayani ga rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG