Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matatar Dangote Ta Zaftare Farashin Litar Dizil Zuwa N1, 020 Daga N1, 075

Matatar mai ta Dangote (Hoto: Facebook/Dangote)
Matatar mai ta Dangote (Hoto: Facebook/Dangote)

A baya-bayan nan, matatar mai zaman kanta ta zaftare tsohon farashin daukar fetur na Naira 950 zuwa 890 “duba da halin da kasuwa ke ciki”.

Matatar man Dangote ta rage farashin litar man dizil din da take tacewa zuwa N1, 020 daga 1, 075 a farashin kamfani.

A cikin wata sanarwa, matatar da aka gina a kan dala bilyan 20 tace ragin wani bangare ne na kokarin da take yi na kyautatawa abokan huldarta dama ‘yan Najeriya baki daya.

“Tun bayan da ta fara tace man dizil a 2024, matatar ta rage farashin fiye da sau 3, daga farashin farko na naira 1, 700 zuwa sabon farashin na yanzu, don haka ta samawa masu masana’antu da kwastomominta sauki baki daya,” a cewar kamfanin.

A baya-bayan nan, matatar mai zaman kanta ta zaftare tsohon farashin daukar fetur na Naira 950 zuwa 890 “duba da halin da kasuwa ke ciki”.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG