Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta tabbatar da cewa daruruwan mutane daga Gwoza da kewaye ne ke gudun hijira zuwa jihar Adamawa da kasar Kamaru, biyo bayan kawanyar da ‘yan Boko Haram suka yiwa garin.
Babban jami’in hukumar, bada agajin gaggawa ta Najeriya, mai kula da shiyar arewa maso gabas, Alhaji Muhammad Kanel, ne ya furta hakan a wata hira da wakilinmu, Ibrahim Abdul azeez.
Yace hukumar na shirye-shiryen kai dauki ga wadannan mutane domin sauwaka masu wasu walhalolin dasuke fuskanta.
Da yake tabbatar da kwararan ‘yan gudun hijiran shugaban karamar hukumar Madagali, Mr. James Watarda, yace karamar hukumar na neman dauki domin taimakawa ‘yan gudun hijiran.
Yau fiye da kwanaki shida kennan da ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka mamaye garin na Gwoza , yayin da jama’a da dama suka tsere da barin wasu akan duwatsu cikin mawuyacin hali.