Bincike ya nuna cewa kaso 99 daga cikin 100 na ‘yan Jamhuriyar Nijar Musulmi ne, wanda wannan ce tasa wasunsu suka tofa albarkacin bakinsu game da sabon hukuncin da kungiyar kasashen Afirka ta Yamma da aka fi sani da Ecowas.
Wanda suka taru suka yanke dokar haramtawa mata sanya nikabi da ke rufe musu fuskarsu baka ganin komai a jikinsu sai idanuwansu. Wanda suna ganin a yadda matsalar tsaro take a kasashen to dole a dauki wannan mataki.
Wata ta bayyana mana yadda suke kallon abin da cewa ba laifi bane in dai har za ayi haka ne don kiyaye lafiya da rayukan al’umma ne. inda wata kuma a nata jawabi tace ai Nijar ba kamar sauran kasashen da suka yanke hukuncin ba ce.
Musamman in suka yi la’akari da cewa wasu kasashen da dama daga cikinsu bas u da yawan musulmin da Nijar ke dashi, amma su wannan doka a kasarsu ai tamkar tauye musu hakkinsu ne da ya kamata su samu na addini.