An dai soma kaddamar da shirin ne a jihar Adamawa, Arewa Maso Gabashin Najeriya, inda mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo yaje ya kaddamar.
Da yake kaddamar da shirin a gandun kiwo na Gongoshi, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, yace manufar shirin daban yake da shirin Ruga da ake ta cece-kuce akai. An kaddamar da shirin ne domin magance tashe tashen hankulan dake wakana tsakanin makiyaya, da manoma.
Yace yanzu kusan jihohi bakwai ne suka rungumi wannan shirin da suka hada da Adamawa, Benue, da Kaduna, Filato, Nasarawa, Taraba, da kuma jihar Zamfara.
Shiko mai masaukin baki gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri yayi amanar cewa shirin zai kawo cigaba ta fannin zaman lafiya, da bunkasa kiwo na zamani, da kuma samar da fahimtar juna.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz.
.
Facebook Forum