Babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Faruk Yahaya, ya ce cancanta ta koshin lafiya za su duba wajen daukan sabbin dakarun kasar.
Janar Yahaya ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyara Cibiyar Duba Cancanta ta sojin Najeriya (NABFC) da ke dajin Falgore a jihar Kano a ranar Talata, inda ake aikin tantance sabbin sojojin da za a dauka a juko na 82.
“Laftanar Janar Yahaya, ya yi kira ga jami’an da ke aikin tantance mutanen, da su yi amfani da abin da suka koya a baya wajen daukan sojojin don ganin an cimma burin aikin.” Wata sanarwa da kakakin yada labarin rundunar sojin kasa ta Najeriya Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar ta ce.
Kazalika Yahaya ya kara da cewa, zai tabbatar an samar da kayayyakin aiki ga cibiyar musamman na horarwa domin a inganta ta.
Yayin da yake jawabi ga Janar Yahaya, Babban Darektan tsare-tsare na daukan sojoji, Manjo-Janar Umar Musa, ya bayyana cewa sama da mutum 3,800 suke kan tantancewa a halin yanzu.
Ya kara da cewa burin cibiyar shi ne a tabbata an dauki ‘yan Najeriya masu koshin lafiya domin a samu biyan bukata.
Najeriya ta jima tana fama da matsalolin rashin tsaro a sassan kasar musamman a arewa maso gabashi da yammaci yayin da rahotanni ke nuni da cewa kasar na fama da karancin sojoji.