Janaral Yahaya na ba da tabbacin hakan ne yayin da ya ziyarci makarantar
don ganewa idonsa abin da ya faru inda ya kira da cewa kada abin da ya faru ya sanyayawa kwamanda da daliban makarantar gwiwa.
Babban hafsan sojojin Najeriyar ya ce hedkwatar mayakan kasar za ta
samar da karin matakai na kara inganta tsaro a makarantar tare da ba da
tabbacin irin hobbasan da a halin yanzu ake na kubutar da hafsan da
'yan bindigar suka yi awon gaba da shi yayin harin.
Tunda farko cikin jawabinsa, kwamandan makarantar Manjo Janar I.M.
Yusuf, ya yi wa babban hafsan hafsoshin bayanın yadda ‘yan bindigan suka yi har suka shiga cikin makarantar da ta kai ga tafka aika-aikar.
Janar Yusuf wanda ya godewa babban hafsan saboda daga martabar
bataliyar gwaji na makarantar ga zuwa cikakkiyar Bataliyar Sojoji tare da samar mata da motocin dake dauke da manyan bindigogi har guda shida wanda ya ce hakan ya kara karfafawa makarantar kwarin gwiwa.