Yau matasa suka kai wata zanga-zanga filin jirgin sama na Malam Aminu, dake Kano suna neman bayani dangane da jirgin dakon kaya na Rasha makare da makamai da jami'an tsaro, suka tsare a filin jirgin sama na Kano a shekaran jiya Asabar.
Wakilin muryar Amurka, Mahmud Ibrahim Kwari ya halarci wurin zanga zangar kuma ya zanta da shugaban gamayyar kungiyoyin matasa na Najeriya, Ibrahim Garba Wala, inda shugaban ya ce dalilin su na fitowa shine domin su nuna damuwar su kan jirgin, da aka tsare, da kuma son jin wadanda ke da hannu akan lamarin.
Jirgin dai, na dauke da jirage masu saukar ungulu biyu, da wata motar Jeep kirar Ford harma da akwatuna dauke da dinbin makamai.
Kuma ya kara da cewa wannan ba shine karo na farko ba, da ake jin cewar an an sami makamai ta filin jirgin Mallam Aminu Kano.
Ibrahim Garba, na mai cewa a wannan tsanani na masifa da ake ciki na kashe kashe ake yiwa ‘yan Arewa, muntabbata cewa al’ummar Najeriya na son jin ta inda maharan ke samun makaman da suke amfani dasu.
Sude gamayyar kungiyoyin matasan na son hukumar Najeriya, ta fito tayi musu bayani a matsayinsu na ‘yan kasa kuma wakilai na al’ummar Najeriya cewa, wannan kayan nawanene .
Jami’an tsaro dai sun fadawa matasan dasu jira za’ayi musu bayani, kasancewar Jami’an na cikin wani taro.