Tsohon minista Sanata Adamu Aliero na daga cikin wadanda suke da dabi'ar canza jam'iyya domin yanzu ma ya jingine PDP wadda yace ba zata yi masa adalci ba ya shige jam'iyyar APC.
Aliero dai ya fito ne daga arewa maso yamma inda aka yi kusan canzaras idan aka duba dawowar Bafarawa da Shekarau PDP daga APC.
Sanata Adamu Aliero yace dimbin magoya bayansu ana nuna masu banbanci. An hanasu shiga cikin zabe. An nahasu katin zama mamba. An mayar dasu sanaiyar ware. Yarjejeniyar da suka yi da kwamitin Tony Anenih ba'a gudanar da ita, abun da ya nuna cewa shugabancin PDP bashi da alkibla.
Da aka gaya masa cewa mutane zasu dauka baya dogon tunane kafin ya canza sheka ganin cewa ya shiga CPC,ANPP da kuma PDP, sai Sanatan yace sabili da dogon tunane ne yasa bai canza jam'iyya sai yanzu. Babu abun da dan siyasa zai yi illa yayi abun da mutanensa suke so.
To saidai dan rajin kare muradun PDP daga arewa maso gabas mai kalubalen tsaro Ado Adamu Bomboi ya yi alwashin hakan ba zai shafi jam'iyyar PDP ba ko sake zaben shugaba Jonathan ba. Yace yakamata mutane su sani karya suke yi. Mutane su sani za'a dinga fada abun da talakawa ke so domin su ci zabe. A wannan karon duk zasu fadi.
Bomboi yace an yi shugabanni tara daga arewa menen suka kullawa Borno. To amma a lokacin Jonathan sun samu jami'a da hanyoyi da dam. Yace ya karbi mutane da yawa daga gwamnatocin Borno da Yobe zuwa jam'iyyar PDP. Yace su babu ruwansu da addinin Jonathan. Domin haka shi zasu bi.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-hikaya.