Rahoton kungiyar da aka fitar cikin makon da ya wuce a Frankfurt, Germany, a wajen taron karawa juna sani na kwana biyu kan yaki da ciwon suga. Masu binciken sun lura cewa yankin Afrika yafi kowanne yanki yawan masu mutuwa da ciwon suga da kashi 81.2% na masu cutar wadda ba’a tantance ba kuma basu san suna da cutar ba.
Kungiyar masu harhada magungunan ciwon sauga da ake kira Sanofi Biopharmaceuticals ce ta shirya taron domin bukin cika shekaru 90 da jinyar ciwon suga da kuma shirye shiryen yin bukin ranar duniya ta bukin cutar sikari na 2014.
Kungiyari tace akwai mutane masu yawa da suke fama da ciwon suga a yankuna da yawa na duniya da suka hada da suka hada da Eurasia, Turkey da tsakiyar yamma, kudancin Asiya, da Afrika. Kamfanin yace mutane miliyan 143 da suke dauke da cutar a duniya suka san suna dauke da cutar suna kumashan magani daga cikin miliyan 371dake dauke da cutar a duniya a cikin wannan shekarar ta 2013.
An kiyasta cewa kimanin mutane miliyan 237 zasu kamu da ciwon suga a wadannan yankunan daga cikin mutane miliyan 552 da zasu kamu da cutar a duniya baki daya.