Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Bukata Ta Musamman Sun Yi Gangami Kan Zaben Najeriya


Hutuna daga cibiyar horas da nakasassu
Hutuna daga cibiyar horas da nakasassu

Hadakar kungiyoyin masu bukata ta musamman ta nakasassu sun gudanar da wani gangamin fadakarwa a Yola, domin yin kira na a gudanar da zabe cikin lumana, kana suka koka da yadda hukumar zabe INEC, ta kasa cika alkawurran data dauka game da nakasassun a zaben da ya gabata.

Masu bukata ta musamman da ake kira nakasassu sunyi jerin gwano a Yola, fadar jihar Adamawa, inda suke neman da a gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.

Mista Bitrus Richard, shine ya jagoranci jerin gwanon da nakasassun suka yi, inda ya bayyana wasu matsalolin da suka fuskanta a zaben shugaban kasa da ya gabata, ya kuma ce hukumar zaben kasar INEC ba ta cika alkawurran data yi musu ba.

Alhassan Ibrahim dake zama jami’in yada labarai na hadakar kungiyar masu bukata ta musamman a Najeriya ya bayyana yadda suka gudanar da zabukan nasu a Najeriya. Ya ce nakasassu sun fito sosai sun yi zabe, sai dai hukumar INEC ba ta cika alkawuran da ta dauka ba.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG