A yau kotun da ke sauraren karar da aka shigar akan Maryam Sanda dangane da zargin kisan mijinta, za ta koma sauraron shari’ar a yankin Jabi da ke Abuja, babban Birnin Najeriya.
Jaridun Najeriya na yanar gizo sun bayyana cewa a zaman da kotun ta yi a baya, ta saka ranar 19 ga watan Maris a matsayin ranar da za a shiga sauraron karar gadan-gadan.
Ana sa ran masu shigar da kara za su gabatar da shaida na farko a tuhumar da ake mata kan kashe mijinta Bilyaminu Bello, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa a shafin yanar gizonta.
A ranar 7 ga wannan wata ne, kotun ta ba da belin Maryam bisa dalilai na rashin lafiya da lauyoyinta suka dangana da yanayi da ta shiga na dauke da juna biyu.
A baya, mai Shari’a Yusuf Halilu, ya ki amincewa ya ba da belin Maryam da aka nema har sau biyar.
Amma daga baya, ya ba da belinta bisa sharadin cewa sai Maryam ta gabatar da mutane biyu da suka mallaki kadarori a Abuja.
Sannan kotun ta bukaci mahaifin Maryam ya saka hanu akan ya amince cewa zai rika gabatar da ita a gaban kotun a duk lokacin da aka bukaci ganinta.
Bayar da belin Maryam ya haifar da cece-ku-ce musamman a shafukan sada zumunta, inda yayin da wasu ke sukar matakin kotun, wasu kuma suke nuna akasin hakan.
A watan Nuwambar bara, aka zargi Maryam da kashe Bilyaminu a gidansu da ke Abuja, bayan da suka samu sabani irin na ma’aurata.
Wasu bayanai sun yi zargin cewa wani sako ta gani a wayarsa dsaga wata budurwarsa da bai yi mata dadi ba.
Maryam Sanda, ‘ya ce ga tsohuwar shugabar bankin Aso Savings, Maimuna Aliyu,
Shi kuwa marigayin da ne ga tsohon shugaban babbar jam’iyar adawa ta PDP na Najeriya, Haliru Bello.
Facebook Forum