Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kotun Daukaka Kara A Nijar Ta Yiwa Dan Jarida Baba Alfa Sassauci


Wadanda suka yi gangamin neman sakin Baba Alfa
Wadanda suka yi gangamin neman sakin Baba Alfa

Yadda Baba Alfa, wani dan jarida dan asalin Mali,wanda ya yi aiki da jaridu masu zaman kansu, ya sa gwamnatin Issoufou ta cafke shi ta kuma gurfanar da shi gaban kuliya har aka daure shi na tsowon shekaru biyu, amma kotun daukaka kara ta yi masa sassauci

Dan Jarida Baba Alfa wanda dan asallin kasar Mali ne, gwamnatin Nijar ta zargeshi da mahaifinsa da mallakar takardun bogi na zama cikin kasar kuma akan zargin ne kotun farko ta yanke masu hukuncin zaman gidan kaso na shekaru biyu.

A yayin zaman da kotun daukaka kara ta birnin Yamai ta zauna akan batun na Baba Alfa da mahaifinsa inda daga karshe ta sassauta daurin da aka yi masu.

Hassan Umaru na cikin lauyoyin Baba Alfa wanda ya tabbatar da sassaucin hukuncin daga shekara biyu zuwa daya. Da wannan sassaucin Baba Alfa da mahaifinsa zasu bar gidan kasao ranar daya ga watan gobe.

Mudi Musa wani jigo a kungiyar 'yan jarida wanda yake cikin 'yan jarida da suka yi cincirindo a harabar kotun ya nuna farin ciki akan sassaucin.

Batun takardun da suka bashi 'yancin 'yan kasa na samun damar ci gaba da ayyukansa, kotun bata ce komi akansu ba. Lauyoyin dake kareshi na ganin kokuwa bata kare ba.

Baba Alfa dan asalin kasar Mali ya yi karatunsa ne a kasarta Nijar kafin ya fara aikin jarida mai zaman kansa. Cikin haka ne ma ya shugabanci kungiyar 'yan jarida a Nijar.

Kamashi da gwamnatin Issoufou ta yi ya haifar da matukar damuwa a wasu kungiyoyin kasa da kasa Ana ganin yadda yake caccakar gwamnatin Issoufou Mahammadou ya sa aka cafkeshi.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG