Jagoran kungiyar nan da ke ikirarin kare muradun tsarin dimokaradiya a Najeriya ne ya bayar da wa’adin kwanaki bakwai ga gwamnatin shugaba Mohammadu Buhari, da ta daidaita al’amurra a cikin kasa, kamar wahalhalun rayuwa da takawa ke fuskanta da rashin Man fetur da kuma tsadar rayuwa, inba haka ba kuma zasu mamaye fadar shugaban kasa ta Aso Rock da kuma yin zaman dirshan.
A gefe daya kuma gwamnatin Najeriya ta mayar da martani ta bakin ministan Matasa da Wasanni Barister Solomon Dalung, wanda yace a karkashin dimokaradiyya kowa nada yancin fadin albarkacin bakinsa, hakan yasa matasan Najeriya ke da ikon nuna rashin gamsuwarsu da dukkan abinda dake faruwa a kasa.
Ministan Matasan ya ci gaba da cewa ga wadanda suka bayar da sakon mamaye fadar shugaban kasa, su sani cewa tabbas dalilan da suka bayar haka suke, sai dai kuma ba yanzu bane aka shiga wannnan matsalar ba, idan kuwa ana maganar zaman lafiya ne to gwamnati ta dauki kwararen matakai, idan har akace gwamnati batayi komai ba to tabbas ba a ayi mata adalci ba.
Daga Ministan ya danganta wahalhalun da ake fuskanta a Najeriya da cewa su nada alaka da yanayin da tattalin arzikin kasar ya shiga, kuma ba gwamnati bace tayi da gangan don gallazawa al’umma ko rashin iya mulki bane, abune da aka tsinci kai ciki kuma ana daukar matakan da yakamata. Matasa na da yancin suyi mamaye ko ina suke so idan har zasu bi doka da oda.
Domin karin bayani.