Suna ganin matakin zai taimakawa gwamnatin Libyan ta dakile barazanar matakan tsaron cikin gida da kuma yaki da 'yan kungiyar ISIS.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry shi ne ya bada sanarwar wannan shawara bayan wani taron da Amurka da Italiya suka yiwa jagoranci.
Mr. Kerry yace Amurka da manyan kasashen yammacin turai ashirye suke su baiwa sabuwar gwamnatin Libya taimakon jin kai da na tattalin arziki da kuma matakan tsaro tare da kayan yaki.
Sabuwar gwamnatin da aka kafa a Libya tana fuskantar kalubale daga kungiyoyin dake gaba da juna a cikin kasar da kuma 'yan yakin sa kai da suke da alaka da kungiyar ISIS, wadanda suka kafa sansani a birnin Sirte, kuma sun yi anfani da sansanin wajen kaddamar da hare-hare akan kasar Tunisia makwafciyar Libya.