Wata mota dankare da nakiyoyi ta kutsa sansanin sansanin sojin na Gao, inda daruruwan sojoji suke ganawa da safe kafin kama aiki.
Kungiyar al-Mourabitoune da take da alaka da reshen kungiyar al-Qaida dake Afrika ta Arewa, ta dauki alhakin harin.
Ministan tsaron Mali Abdoulaye Idrissa Maiga, yace harin na jiya Laraba yana cikin yakin da bashi da suna.
Sojojin suna ciki rundunar hadin gwiwa da ya hada sojojin gwamnati da na rundunar mayakan tsohuwar kungiyar yan tawayen Azbinawa da suke sintiri da nufin aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar da nufin wanzar da zaman lafiya a Mali.
Kungiyar yan tawayen Azbinawa ta yi amfani da damar da suka samu na juyin mulkin kasar a shekarar 2012, suka kwace yankin arewacin kasar na takaitaccen lokaci, kafin kungiyar ta’adda mai alaka da a-Qaidan ta koresu daga yankin.