Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Al'Qaida Ta Dauki Alhakin Harin Sansanin Sojojin Gao A Mali


Sojojin Mali da suka jikata a harin na Gao jiya Laraba
Sojojin Mali da suka jikata a harin na Gao jiya Laraba

Kungiyar Al’qaida ta dauki alhakin harin kunar bakin waken da da aka kai jiya Laraba a sansanin sojojin kasar Mali dake arewacin kasar, wanda yayi dalilin mutuwar sojoji a kalla 60, da suka hada da wasu tsoffin ‘yan tawaye, yayinda wasu 115 suka samu raunukka iri daban-daban.

Rahotanni sun bayyana cewa wata mota ce da aka shake ta da boma-bomai ta kutsa kai cikin barikin sojan dake garin Gao, lokacin da daruruwan sojojin ke gudanar da taron su na safe.

Da yawan wadannan sojojin da wannan lamarin ya rutsa dasu suna cikin sojojin hadin gwuiwa ne, wadanda suka hada da sojojin gwamnati da tsoffin ‘yan tawaye, wadandasune suka hadu suka samar da tawagar dake gudanar da sintiri domin ganin an aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimmawa a kasar Mali a cikin shekarar 2015.

Ministan harkokin wajen kasar na Mali Abdoulaye Diop ya bayyana wannan harin a matsayin abin kaico, tir da dabbaci.

Ministan yace wannan ba zai sa kasar tayi kasa a gwuiwa ba ko kuma janye hankalin su daga kokarin da gwamnatin keyi na ganin ta samar da zaman lafiya, tare da daukar matakin da suke ji ya dace a kan mutanen nan da suke kokarin ganin sun kawo wa wannan kokarin zaman lafiya cikas.

Diop, wanda ke magana sailin da yake jawabi wajen wani taron da Majilisar DinkinDuniya ta shirya game da kasar ta Mali, yace Mali zata yi zaman makoki na kwanaki ukku domin jimamin wadanda suka rasa rayukan su kana zata yi duk abinda ya dace domin cafko wadanda suka aikata wannan danyen aikin domin a hukunta su.

XS
SM
MD
LG