Taron akan matsalar bakin haure ya tattaro malaman jami'o'i arba'in na kasashen duniya da shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu da jakadun kasashe daban daban.
Taron ya mayarda hankali ne kan yadda matsalar bakin haure ke cigaba da yin kamari tare da nemo bakin zaren warware matsalar..
Ministan ilimi mai zurfi na kasar Nijar Muhammad Ben Umar shi ya jagoranci bikin bude taron. A cikin jawabinsa ya bayyana yadda bakin haure ke mayarda yakin na Agadez wurin zuwa Turai ba kan ka'ida ba.
Inji ministan alakalumma da aka tattara sun nuna cewa mutane kimanin 120,000 suka yi anfani da yankin na Agadez zuwa Turai daga shekarar 2015 zuwa 2016. Lamarin da ya mayar da yankin Agadez tamkar matattara ga bakin haure. Yace saboda haka matsalar bakin hauren ta dauki hankulan 'yan Nijar musamman ma mahukumta.
Taron ya kunshi jakadun kasashen Turai da na Afirka domin haka akwai wadanda zasu sa hankali a taron domin su yi anfani dashi a kasashensu.
Amma Farfasa Mukhtar Umaru Bunza na Jami'ar Usmanu Dan Fodio dake Sokoton Najeriya cewa yayi muddin ana son a kawo karshen matsalar bakin haure to ya zama wajibi a yi anfani da abubuwan da aka cimma a taron. Yace matsalar bakin haure ta shafi duniya gaba daya.
Ga rahoton Yusuf Abdullahi da karin bayani.