Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Nijar Hukumar Cinikayya Ta Kona Gurbatattun Kayan Masarufi A Damagaran


 Kone kayan masarufi a Damagaran
Kone kayan masarufi a Damagaran

A wani yunkuri na kare lafiyar al'ummarta, hukumar cinikayya ta jamhuriyar Nijar ta soma bin shaguna tana kwace gurbatattun kayan masarufi tana konesu.

Kusan kowane irin kayan masarufi kama daga madarar gwangwani zuwa taliya suna cikin kayan da aka kone.

Hukumar Cinikayya ta yankin Damagaran ta kwace kayan a wasu shaguna dake birnin garin.

Namata Insha, daraktan hukumar cinikayya a Damagaran
Namata Insha, daraktan hukumar cinikayya a Damagaran

Daraktan hukumar Namata Insha yace zasu cigaba da aikin har sai sun tabbatar ana sayarwa jama'a kayan masarufi nagatattu domin kiyaye lafiyar jama'a. Sun bukaci jama'a su basu goyon baya akan aikin da su keyi a kuma duk lokacin da suka fita yin aikin.

Hukumar Cinikayya ta Niger ta kone gurbatattun kayan masarufi da ta kwace daga shaguna
Hukumar Cinikayya ta Niger ta kone gurbatattun kayan masarufi da ta kwace daga shaguna

Yace sun yi aikin ne da goyon bayan wasu hukumomin gwamnati irin su 'yansanda da kwastan da masu kula da shige da fice.

Malam Isa Musa da ya jagoranci bikin kone kayan ya kira 'yan kasuwa su dinga kula da kayan da suke sayarwa al'umma domin a kiyaye kamuwa da cututtuka.

Yace hukumar cinikayya nada ikon shiga shaguna su duba kayan dake ciki idan kuma sun ga wanda wa'adinsa ya kare wajibi ne su kwace su kuma kone.

Ga rahoton Tamar Abari da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG