Taron kwanaki ukun da ya tattauna hanyoyin nemo maslaha game da abubuwan dake kawo rikice-rikice da kuma hare-hare ya cimma matsayar yada fahimtar juna tsakanin mabiya addinai a Najeriya.
Pastor James Mobel Wuyeh shine jagoran cibiyar da ta shirya wannan taro kuma ya an gayyato malaman makarantun Islamiya da masu koyarwa a coci coci da kuma manya manyan malamai masu jama’a.
Yace dalilin shirya wannan taro shine domin a takawa masu tsatsauran ra’ayi na addini, su san yadda zasu dinga sarrafa maganganu musamman su daina shige iyaka. Kuma domin a dawo da hankalin wadanda tunaninsu yayi zurfi ta wannan fannin.
Ya kuma kara da cewa su kara jan hankalin malamai su koyar da darrusa da zasu hana mutane shiga halin wuce gona da iri a addini.
Mahalarta taron kwanaki ukun da aka yi a Kaduna sun ce irin wannan taro na iya dinke barakar da ke tsakanin mabiya addinai.
Babban burin wannan taro dai shine nuna wa malaman addinai muhimmancin da ke da akwai wajen ganin sun janyo mabiya don ganin basu shiga ta’addanci ko tada hankulan al’umma ba.
Dama dai wasu masana harkokin tsaro na ganin dole al-umma su rinka shinfida shirin fahimtar juna don magance matsalolin tsaro maimakon zubawa gwamnati ido duk lokacin da rigima ko rikici ya taso.
Saurari cikakken rahoton Isa Lawal Ikara:
Facebook Forum