Hukumar kula da ilimi da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ce ta kirkiro da wannan ranar malaman makaranta tun a shekarar 1994, tare da zimmar tattauna batutuwa da suka shafi yanayin aikin malamai da matsayin ilimi a duniya.
A wannan rana ne ake ba da shawarwari a kan hakkokin da suka rataya a wuyan malamai da matsayin iliminsu da batun karo ilimi da daukar su aiki da batun koyo da kayarwa.
Haka zalika rana ce da ake yabawa da kokarin da malamai ke yi ga ci gaban al’umma.
Bikin wannan shekarar ta 2020 na zuwa ne a lokacin da annobar COVID-19 ta kara haifar da matsaloli masu yawa a kan wadanda ake fama dasu wurin kokarin fadada tsarin ilimi a duniya.
A kasashe masu tasowa, malamai kan yi amfani da wannan rana wurin sake duban bukatunsu domin gabatar da su ga mahukunta tare da manufar magance musu matsaloli da suke fuskanta.
Mataimakin sakataren kungiyar malaman kwantaragi a jamhuriyar Nijar, Cherif Issouhou ya ce a wannan rana ta biyar ga watan Oktoba, suna haduwa domin bullo da sababbin salon koyarwa da zai amfani harkar ilimi a kasar.
Issouhou ya ce sha'anin ilimi ya tabarbare a jamhuriyar Nijer, malamai suna fama da koke koke a kan alkawura da ake ta yi musu amma ba'a cikawa musamman malamai ‘yan kwantaragi ba'a basu albashi kan lokaci.
Ya kara da cewa akwai abokan aikin su da har yanzu ba'a ma fara biyansu a matsayin malamai ba.
Mataimakin sataren kungiyar malaman kwantarin ya kuma ce batun ajujuwan karatu ma wani babban kalubale ne da ake fama dashi a birane da kauyuka a jamhuriyar Nijer.
"Ambaliya da ta abkawa mutane a birnin Yamai ta sa an tsugunar da mutanen a azuzuwan makarantu kana har yanzu ba'a kwashe su ba balle a sami inda za'a yi karatu.
Ga tattauanawar da Souley Moumouni Barma ya yi da mataimakin sakataren kungiyar malaman kwantaragi a Nijer, Cherif Issouhou:
Facebook Forum