Hukumar zabe ta kasar Uganda zata fara amfani da na’urar tantance masu jefa kuri’a – wato na’urar da ke amfani da halittar mutum ta tantance shi – wadda za a yi amfani da ita wajen sabunta rajistar masu kada kuri’a gabanin babban zaben da za a gudanar wannan shekarar,inji mai magana da yawun hukumar zaben Jotham Taremwa.
Ya musunta rahotannin dake cewa hukumar zaben ba ta da kudin da take bukata wajen shirya zabe cikin watanni goma, Teremwa yace, hukumar zaben tana bukatar dalar Amurka miliyan 90 don gudanar da zabe. Gwamnati ta bayar da miliyan 67, amma bata bayar da ragowar ba.
Wasu ‘yan adawa na nuna damuwarsu kan cewar jam’iyya mai ci a yanzu NRM ka iya amfani da damar rashin kudin zaben wajen aiwatar da magudin zabe, domin tabbatar da shugaban kasa Yowerri Museveni yaci zaben mai zuwa.
‘Yan jam’iyyun adawa na bukatar sake fasalin zaben kasar, bayan da aka zargi hukumar zaben da nuna banbanci kan ‘dan takarar NRM mai ci a yanzu. Suna kuma bukatar sake rajistar zabe da ake amfani da ita a yanzu haka.