Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majo Hamza Al-Mustapha yace ba saboda zargin kashe Kudirat Abiola ake tsare da shi ba.


Sojojin Najeriya suna sintiri a kan hanya.
Sojojin Najeriya suna sintiri a kan hanya.

Major Hamza Al’Mustafa ya bayyana cewa ba domin kashe Kudi Abiola ake tsarae da shi ba. Bisa ga cewarshi, ana tsare da shi ne sabili da zunzurutun kudin da aka fitar daga babban bankin Najeriya domin bada toshiyar baki ga wadanda ake ganin zasu iya tada hayaniya lokacin da aka ce Mashood Kashimawo Olawale Abiola ya rasu.

Major Hamza Al’Mustafa ya bayyana cewa ba domin kashe Kudi Abiola ake tsarae da shi ba. Bisa ga cewarshi, ana tsare da shi ne sabili da zunzurutun kudin da aka fitar daga babban bankin Najeriya domin bada toshiyar baki ga wadanda ake ganin zasu iya tada hayaniya lokacin da aka ce Mashood Kashimawo Olawale Abiola ya rasu.

Tsohon mai tsaron shugaban kasa marigayi janar Sani Abaca manjo Hamza Al’mustafa shine ya fadawa kotu haka a lokacin da yake amsa tambayoyi daga lauyan sa, yace tun lokacin da marigayi tsohon shugaba janar Sani Abaca ya rasu aka nemi a kashe MKO Abiola amma shi manjo Al’mustafa shine ya canza masa wuri amma daga baya aka bishi can aka kashe shi.

Majo Hamza Al- Mustapha ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa na wancan lokacin janar Abdulsalam Abubakar domin kuma shine ya bada umurni a fidda kudi har dalar Amirka miliyan dari biyu da Fan miliyan saba’in da biyar da wadansu naira miliyan dari biyu domin rarrabawa mutanen da ake ganin cewa zasu tada kayan baya game da rasuwar Chief M.K.O. Abiola.

Manjo Mustafa yace shine ya taimakawa janar Abdulsalam Abubakar ya zama shugaban kasa a wannan lokacin domin shi kadai ne yasan cewa janar Sani Abaca ya rasu kuma a wannan lokacin yana da damar canza tarihin siyasar Najeriya amma yaki yayi hakan domin ganin cewa bukatar kasa na gaba kafin nasa.

Majo Hamza Al-Mustapha yace shi kansa Janar Abdulsalam ya amince cewa shine ya taimake shi ya zamo shugaban kasa kuma yace sakayyar da zaiyi masa shine ya tura shi kasar Pakistan domin ya huta da sunan kwas amma ya umurce shi da ya fara zuwa Enugu tukunna amma kuma kwaran sai ya umurci kwamandan sa na Enugun ya maka masa takardan cewa ya gudu ya bar bakin aiki alhali duk da yake an san an tura shi garin Enugu.

Bayan kwanaki uku kuma sai aka kama shi. Manjo Mustafa yace tun daga wannan ya shiga shan akaba daga wannan kwamitin binciken zuwa wancan da sunan juyin mulki ko kuma kashe wane ko wance, wanda har bisa ga lokacin da yake bada wannan shaidar a kotu yake kan shan wahala.

Tsohon mai kula da tsaron marigayi tsohon shugaban kasa janar Sani Abacha yace har lokacin da aka kai shi birnin ikko anyi yunkurin kashe shi sai dai da yake kwanan sa na gaba yasa aka samu rashin jittuwa tsakanin Nuhu Ribadu da Mike Okiro wanda shine kwamishinan Yan sandar Jihar Legas na wancan lokacin, ya kekasa kasa yace sam bai yarda a kashe shi yana hannun sa ba.

Manjor Mustafa yace wannan ne yasa aka canza shi Mike Okiro daga Legas a wannan lokacin. Majo Hamza Al-Mustapha yace duk wadanda aka kawo kotu domin su bada shaidar karya game dashi daga baya sun bayyana cewa an biya su ne domin su bada shaidar karya. Majo Hamza Al-Mustapha yace yana da hotuna ko kuma bidiyo domin tabbatar da dukan abinda ya fada a gaban kotun, wanda suna cikin abubuwan da tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalam Abubakar yasa aka kwace masa sai dai yace har yanzu yana da wadansu.

Bayan ya dauki tsawon sama da sa’oi hudu yana bada shaida Majo Al’mustafa ya daga Kur’ani mai mai tsarki kana yayi rantsuwa da ALLAH kuma azumin dake bakin sa yace idan abinda ya fadi game da tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalam Abubakar karya ne Kuranin yaci shi.

Daga karshe yace duk wanda ya kira cikin wannan batun yana da madogaran yin hakan kuma inda duk ya kasa kare kansa to ya amince ayi masa hukuncin duk da ya dace ayi masa ba tare da sassauci ba.

Mai shari’a Mojisola Dada ta dage sauraron kara zuwa ranar uku ga watan nan na Agusta inda ake kyautata zaton majo Al’Mustafa zai ci gaba da bayanai ya kuma gabatar da hotunan da kuma bidiyon da har yanzu yake dasu kamar yadda ya bayyanawa kotu.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG