Hukumomin Britaniya su na nazarin sahihancin wani faifan bidiyon dake ikirarin nuna wani dan Britaniya da wani dan kasar Italiya wadanda aka sace a Jihar Kebbin Najeriya a cikin watan Mayu.
Ma’aikatar harkokin wajen Britaniya ta fada yau alhamis cewa jami’ai su na nazarin wannan bidiyo, inda a ciki mutanen biyu suka yi ikirarin cewa kungiyar al-Qa’ida ce ta sace su.
An aika da wannan bidiyo zuwa ofishin kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, a kasar Ivory Coast, amma kuma ba a nuna shi ma jama’a ba.
‘Yan bindiga sun sace mutanen biyu ranar 12 ga watan Mayu daga gidan da suke ciki a Jihar Kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya. Dukkan mutanen biyu injiniyoyi ne na wani kamfanin aikin gine-gine na kasar Italiya.
An sha sace mutane a yankin Niger Delta mai arzikin man fetur a kudancin Najeriya, amma irin wadannan sace-sace na mutane ba abu ne da aka saba ganinsu a yankin arewacin Najeriyar ba. A cikin ‘yan shekarun nan, an sace ‘yan kasashen waje da dama a kasar Nijar mai makwabtaka da Najeriya daga arewa. Jihar Kebbi ta Najeriya tana bakin iyaka da kasashen Nijar da jamhuriyar Benin.